Banki Moon ya bayyana haka ne a wani ziyarar aiki da ya kai birnin Adis Ababa cibiyar kungiyar tarayyar Africa a ranar litinin da ta gabata, inda ya gana da shugaban bangaren zartarwa na kungiyar Malama Dlomina Zuma, ya kuma kara da cewa cutar ta Ebola tana yaduwa da sauri fiye da yadda kasashen duniya suke yakarta. don haka akwai bukatar kasashen nahiyar su taimakawa kasashen Guinea Conakry, Liberia da Kuma Salio wadanda suka fi fama da cutar don shawo kanta.
Tare da babban sakataren a wannan ziyarar akwai shugaban Bankin duniya
Jim –Yung Kim, wanda ya bayyana cewa kasashen da suke fama da wannan cutar suna bukatar karin likitoci da jami’an kiwon lafiya fiye da 5000 don dakatar da yaduwar cutar. Amma ya bayyana damuwarsa kan inda wadan nan likitoci da jami’an kiwon lafiya zasu fito a duniya.
Har’ila yau a nata bangeren shugaban bangaren zartwarwa na kungiyar tarayyar ta Africa Malama Zuma ta ce kasashen nahiyar sun yi alkawarin tura jami’an kiwon lafiya wadanda suka hada da likitoci da jami’an jinya fiye da 2000 zuwa wadan nan kasashe guda ukku na yammacin Africa, sai dai bata bayyana lokacin yin haka ba.
Cutar Ebola dai ta fara bullowa ne a kasar Guinea Conakry a farkon wannan shekarar, daga can kuma ya yaduwa zuwa kasashen da suke makobtaka da ita wadanda suka hada da Liberia da kuma Salio. Hukumar Lafiya ta duniya dai ta bayyana cewa cutar ta kama akalla mutane dubu 10 ya zuwa kuma yanzu sannan ta kashe kashe kusan rabinsu.
A wani bangare kuma shugaban hukumar bada agajin gaggawa na tarayyar Turai (ECHO) a kasar Mali Mr Patrick Borbir ya bayyana cewa tsari bai daya na yaki da cutar tsakanin kasashen duniya, yana daga cikin abubuwan da zasu taimaka wajen shawo kan yaduwar wannan cutar.
Gwamnatin kasar Amurca dai ta dauki sabbin matakai na hana yaduwar cutar a kasar, ta hanyar killace duk wani ba Amurke da ya dawo kasar daga yammacin Africa na tsawon kwanaki 21 don gudanar da bincike da kuma tabbatar da cewa bas a dauke da wannan cutar kafin a kyalesu su shiga mutane. ABNA